Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
Imam Ibnil Qayyim (Rahimahullah) yace:
“Salatin Annabi (SAW) yana daga sababin amsa addu’a, da gafarta zunubai, da samun kariyar Allah, da kusantuwa zuwa ga Allah (SWT).” [Duba littafin Jila’ul Afham]
Imam Ibn Al-Jawziy (Rahimahullah) yace:
“Idan Allah yana nufin bawansa da alkhairi, sai ya saukake masa yin salatin Annabi (SAW).” [Duba littafin Bustanul-Wa’izin]
Sheikh Ibn Baz (Rahimahullah) yace:
“Salatin Annabi (SAW) sababi ne na shiriyar bawa da kuma rayuwar zuciyarsa.” [Duba Al-Fatawa]
Imam Al-hafiz Ibn Hajar (Rahimahullah) yace:
“Yana daga manyan hanyoyin kawar da annoba idan ta sauka, yawaita salatin Annabi (SAW).” [Duba Bazlul Ma’un]
“Idan yini ya kasance na Jumu’ah, to ku yawaita salati a daren Jumu’ah da yinin Jumu’ah.” [Duba Sahihul-Jami’]
Sheikh Ibn Uthaimin (Rahimahullah) yace:
“Bana tunanin wanda yake son Allah da Manzonsa zai taɓa iya daina yiwa Manzo (SAW) salati har abada.” [Duba Liqa’ al-Babul Maftuh]
Imam Ash-shafi’i (Rahimahullah) yace:
“Ni ina son a yawaita yiwa Manzo salati a koda yaushe, ina tsananta hakan a yini da kuma daren Jumu’ah.” [Duba Al’um]
Wassalamu Alaikum,
Dan uwanku: Imam Murtadha Muhammad Gusau. Litinin, 02/01/2023 ~ 08038289761.
Discussion about this post