Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta kam wani faston cocin ECWA mai suna Bitrus Albarka da aka samu da laifin kitsa sace da kansa.
DPO din ofishin ‘yan sandan dake Nasarawa Gwong Musa Hassan da ya sanar da haka ranar Alhamis ya ce rundunar ta kama faston bisa ga zargin hannnu da yake dashi da wadanda suka yi garkuwa da shi bayan an sake yin garkuwa dashi karo ta biyu.
“Sakamakon binciken da muka gudanar ya nuna cewa a karon farko mutanen cocin sun tara naira 400,000 kudin fansar faston wanda aka biya ranar 14 ga Nuwamba sannan bayan an sake yin garkuwa da shi karo na biyu aka biya kudin fansar sa naira 200,000.
“Sai dai rundunar ta gano cewa wadannan kudade sun shige aljihan faston ne ba wasu yan bindiga ba.
Hassan ya kuma kara da cewa rundunar ta gano cewa faston ya kona motoci biyu kirar marsandi da Toyota sannan da Keke guda daga na wasu fastoci da yake aiki tare da su a cocin.
“A dalilin haka ya sa muka kamo faston inda ya shaida mana cewa shi ya hada baki da wasu mutane domin a yi garkuwa da shi saboda ya samu kudaden da zai biya basukan da ake bin sa.
“ Faston ya kuma ce ya kona wadannan motoci saboda kiyayyar dake tsakaninsa da daya daga cikin fastocin cocin.
Ya ce Albarka ya nemi afuwar fastocin cocin da sauran mutane cewa ya bi hudubar shaidan ne.
Hassan ya ce Albarka ya bayyana wa jami’an tsaron cewa Baruk Mailale, Nathaniel Bitrus mazaunan unguwan Yelwan Zangam dake karamar hukumar Jos ta Arewa da wani Aye daga Jalingo jihar Taraba ne wadanda ya hada baki da su domin a yi garkuwa da shi.
Ya ce Baruk Mailale da Nathaniel Bitrus na tsare a ofishin ‘yan sanda.
Discussion about this post