‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Kefas Ishaya faston cocin katolika na St Monica dake Ikulu-Pari a masarautar Chawai dake karamar hukumar Kauru a jihar Kaduna ranar Alhamis.
Maharan sun yi garkuwa da Ishaya ne bayan basu samu dauke babban faston da suka zo nema ba fada Joseph Shekari wanda a ranar da maharan suka kawo wa gidansa hari ba ya nan a gida.
Idan ba a manta ba a watan Fabrairu 2022 mahara sun yi garkuwa da Shekari yanzu a 2023 kuma maharan sun sake dawowa domin kara waskewa da shi amma a wannan karon basu iske shi gida ba.
‘Yan cocin na zargin cewa maharan sun kawo wa gidan fada hari ne saboda su saci kudin godiya da cocin ta yi ranar Lahadin da ta gabata saboda a shekarar bara ma haka suka yi.
Shugaban kungiyar kabilar Ikulu na coci Sunday Bage ya ce maharan sun kai wa gidan fadan hari da misalin karfe tara da rabi na dare.
“ Allah ya sa a ranar da maharan suka kai wa gidan hari Shekari baya nan da hakan ya sa suka tafi da Ishaya tare da wayar sa.
“ Tun da abin ya faru muke kiran wayar salulan Ishaya amma ba a amsawa.
“ Maharan sun shigo suna ta harbi ta ko ina inda suka bi ta cikin harabar cocin, makaranta sannan suka shiga gidan faston domin kama fadan.
Makwabta sun bayyana wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN cewa ta Katanga maharan shiga gidan fadan.
Sun ce maharan sun balla kofar shiga gidan bayan da suka harbi kofan da duwatsu da harsasai.
Discussion about this post