‘Yan bindiga sun yi garkuwa da dagacen kauyen Ummadau dake karamar hukumar Safana Barau Muhammadu da wasu mutum biyu.
Maharan sun sace wadannan mutane ne a ranar Laraba a hanyar su ta zuwa hedikwatar karamar hukumar Safana domin taron kamfen na jam’iyyar APC.
Wani mazaunin Safana Abubakar Safana ya ce maharan sun waske da Muhammadu, da Wani da suke aiki tare sannan da wani dattijo kafin su karisa hedikwatar karamar hukumar.
“Na Yi magana da dan dagacen kauyen inda ya bayyana mun cewa maharan sun kira su amma duk abin da ya faru zan fada maka.
Har yanzu babu Wanda ke da masaniyar sunayen mutum biyu din da maharan suka waske da tare da Muhammadu amma Safana ya ce dattijon dake tare da su limamin kauyen ne.
Ya ce shekara daya kenan da mutane basu bin hanyar Ummadau zuwa Safana saboda tsananin garkuwa da mutane da ake yi a hanyar.
Zuwa lokacin da aka hada wannan labari kakakin rundunar ‘yan sanda jihar Katsina Gambo Isa bai ce komai ba.
Karamar hukumar Safana na daga cikin kananan hukumomin dake fama da yawan hare-haren ‘yan bindiga domin tana kusa da dajin Rugu da mahara ke zama ciki.
Sauran kauyukan dake kusa da Safana da suka hada da Jibia, Kurfi, Batsari and Danmusa suma na fama da hare-haren ‘yan bindiga a jihar.
Discussion about this post