Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa yana shirin watsar da tafiyar Tinubu ya tsunduma rundunar Atiku.
Jaridar Tribune ta buga cewa gwamna Yahaya Bello na Kogi na shirin watsar da Tinubu ya koma tafiyar Atiku Abubakar na PDP.
Rahoton ya yi ikirarin cewa Mista Bello yana fargabar cewa Mista Tinubu na iya marawa James Faleke baya a 2024 a takarar gwamnan jihar Kogi
Sai dai kuma fadar gwamnatin Kogi ta fitar da sanarwar cewa babu wannan batu a tsarin gwamna Bello.
Darektan yaɗa labarai na jihar Kingsley Fanwo, ya bayyana cewa wannan labarin ƙanzon kurege.
” Gwamna Yahaya Bello na tare da Tunubu kuma yana cikin tafiyar tsindum kuma akullum tare da shi ake gwagwarmayar tallata Tinubu a jihar Kogi domin samun nasarar sa a zaɓe mai zuwa.
Fanwo ya ce jihar Kogi ta APC ce kuma Tinubu ne kawai a gaban gwamnan jihar kuma shi yake wa aiki.
Discussion about this post