Tsohon babban hafsan sojojin Samana Najeriya, AM Sadique Abubakar ya sha alwashin maida jihar Bauchi sabuwa fil ya idan ya yi nasara a zaɓen gwamna na watan Maris.
Sadique ya bayyana cewa zai sauya fasalin jihar ta yadda ƴan jihar za su rika alfahari da jihar su ba kamar yadda ake mulki yanzu ba.
A wurin taron kaddamar da daftarin ayyukan da gwamnatin sa zata yi idan ta yi nasara a zaben watan Maris, Sadique ya ce babban abinda zai fi maida hankali a kai shine inganta fannin kiwon lafiya, Ilimi da tattalin arzikin jihar.
” Yanzu haka akalla mata 1,549 ciki 100,000 ne suke mutuwa a lokacin haihuwa a jihar kamar yadda alkaluma suka nuna. Haka kuma jihar ce ke can kasa wurin karincin yara da ke zuwa makarata dake da kasa da 29 cikin 100.
” Idan muka zo za mu canja wannan tsari mu warware matsalolin nan cikin gaggawa.
Manyan baki da suka halarci wannan taro sun haɗa da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, wanda a jawabin sa ya ce yana gaba wajen tabbatar wa mutanen Bauchi cewa ba za du yi zaɓen tumun dare ba.
Ministan Shari’a Abubakar Malami, Tsohon babban hafsan sojojin Najeriya, Tukur Burutai duk sun halarci taron kuma sun bada gudunmawarsu ga ɗan takarar.
Sadique zai gobza da Bala Mohammed Ƙauean Bauchi, wanda ya ke ciki tsaka mai wuya a daidai wannan lokaci da siyasa ta kunno kai.
Dalili kuwa shine ya na da matsala a jam’iyyar sa ta PDP, inda basu tare da ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ‘ Atiku Abubakar, sannan kuma a bangare APC ga dakaren soje na jiran sa.