‘Yan ta’adda sun sace dalibai hudu na Kwalejin Fasaha ta Lafiya ta Jihar Zamfara, Tsafe da ‘yan uwansu mata da suke dawowa daga daurin auren abokin aikinsu a ranar Lahadi.
Daliban na komawa Kaura Namoda daga Birnin Magaji da ke Arewacin Jihar Zamfara, ‘yan ta’addan sun far wa motocin da suke ciki inda suka yi awon gaba da akalla mutane 18 – daliban hudu da mata uku da wani mutum guda tare da ‘yan uwansu guda uku.
PREMIUM TIMES ta gano cewa jami’an tsaro da gwamnati na ta kokarin boye maganan garkuwar saboda akwai dalibai cikin wadanda aka sace. Sai dai wani dan gidan daya daga cikin wadanda abin ya rutsa da su ya ce tuni har an fara tattaunawa da ‘yan ta’addar.
Shi ma Shugaban Kwalejin, Yusuf Maradun, ya tabbatar da aukuwar abin ga PREMIUM TIMES. Sai dai ya ce sace yaran bai faru a makarantar ba, kuma iyalan wadanda aka kashe din ba su sanar da makarantar ba.
“ Sun tashi ne daga garuruwan su daban-daban a lokacin hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara domin bikin auren daliba daya a Birnin Magaji inda aka sace su.
Ya bayyana sunayen daliban kamar haka: Jamila Yahaya, Umma Sani – Umar, Hafsat Dahiru – Kura da Abdullahi Umar da ’Yan’uwan uku: Aisha Yahaya, Nabila Dahiru da Umma Abubakar.
“’Yan ta’addan sun kira mu, sun ce sun kira wasu ‘yan uwan sauran daliban, sun bukaci a biya naira miliyan 20 kudin fansa ko daga wurin su.Haka nan nima abinda suka bukaci in biya kenan.” in ji wani dangin ɗaya daga cikin ɗaliban.
Sai dai kuma ya ce mahaifin amaryar ya bukaci ‘yan uwa da su daina tattaunawa da ‘yan ta’addan a daidaikunsu. Su bari su rika magana da ‘yan ta’addan a tare.