Rundunar sojin Najeriya dake aiki a karkashin ‘Operation Forest Sanity’ sun kashe ‘yan bindiga biyu a karamar hukumar Chikun dake jihar Kaduna.
Kwamishinan tsaro na jihar Samuel Aruwan ya sanar da haka a wata takarda da ya aika wa namema labaraia garin Kaduna.
Aruwan ya ce dakarun sun kashe ‘yan bindigan bayan da suka yi batakashi da su a hanyar Kaboresha zuwa dajin Rijana zuwa Kuzo zuwa Kujeni zuwa Gwanto zuwa Kachiya.
Ya ce dakarun sun kwace babura uku na maharan.
“Dakarun sun Kuma kai wa maharan hari a maboyar su dake hanyar Kutura zuwa Rijana sai dai kafin dakarun su iso wurin maharan sun gudu cikin daji.
“Dakarun sun kama babura uku da kayan sojoji da dama a maboyar maharan.
“Gwamnati za ta ci gaba da kai wa maharan hari sannan ta yi kira ga mutane da su rika taimakawa jami’an tsaro da bayanan da suka san zai taimaka musu wajen gudanar da aikinsu.
Bayan wannan nasara da sojoji suka samu Gwamnan jihar Nasir El-Rufa’I ya jinjina namijin kokarin da dakarun suke yi sannan ya hore su da su kara zage damtse domin ganin an gama da ‘yan bindiga a jihar.
Har yanzu dai jihar Kaduna na fama da hare-haren ƴan bindiga a wasu yankunan jihar musamman kananan hukumomin Birnin Gwari da da Chikun ɗin.
Discussion about this post