Wata mata mahaifiyar ‘yar shekara 17 ta kai kara a kotun dake sauraron kararrakin cin zarafin mata da yara kanana dake Ikeja jihar Legas kan yadda wani fasto mai suna Chris Mcdouglas ya rika lalata da ‘yarta na tsawon shekara uku bata sani ba.
Kotun ta gurfanar da fasto Mcdouglas Shugaban cocin ‘Peculiar Generation Assembly’ bisa laifuka 9 da suka hada da cin zarafi da yi wa ‘yar shekara 17 fyade.
Sai dai kuma fasto Mcdouglas ya musanta wadannan zarge zarge da ake masa.
Bayan hujojin da fannin dake gurfanar da masu aikata laifuka irin haka ta gabatar da hujojin da mahaifiyar yarinyar ta bada wanda ta ce faston ya fara lalata da ‘yarta tun shekarar 2027 zuwa 2020.
Ta ce faston ya kan yi lalata da ‘yarta a wani gini dake kusa da cocinsa, Otel sannan da gida a duk lokacin da bata nan a gida.
“Mcdouglas da na amince da ya kan zo gida na ya fita tare da ‘yata zuwa coci saboda tana da baiwar muryar waka.
“Ashe ban sani ba idan suka fita sai ya kai ‘yata Otel ya kwana da ita. A wasu lokuttan ya danne ne a bayan cocin sa ko kuma idan dare ya yi ya lallabo ya shigo gida na ya yi lalata da ‘ya ta lokacin da nake barci.
Mahaifiyar ta ce ta tunkari faston da maganar yi wa ‘yar ta fyade ya rika rokon ta yana cewa hudubar saidan ne.
“Da na tunkari faston sai ya fashe da kuka ya nemi afuwa daga wurina cewa ya bi hudubar shaida ne.