Kasuwar cinikin sabbin naira ya buɗe ya Tashoshin mota a Zariya jihar Kaduna a karshen wannan mako.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya ruwaito yadda aka buga harkallar cinikin sabbin naira a tasahoshin mota na Zariya.
Wani ɗan kasauwa mai suna Mohammed Bello, ya ce suna saida bandir ɗin naira 200, wato dubu ashirin naira 30,000.
Haka kuma bandir daga n naira 500, naira dubd saba’in, sai kuma bandir din naira 1000, naira dubu ɗari da talatin.
Harkallar kasuwancin sabbin takardun kudin ya karaɗe wasu sassan kasar nan ciki harda babban birnin tarayya, Abuja.
Sai dai kuma Mohammed bai faɗi inda suke samun kuɗaɗen ba su kuma su saida.
Discussion about this post