‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wani tsohon soja mai muƙamin konel tare da iyalen sa a Yandoto dake karamar hukumar Tsafe.
Maharan sun yi garkuwa da Rabi’u Wanda a da shine kwamandan hukumar kula da tsara ta jihar Zamfara, Zarota tare da ‘ya’yan sa biyu da abokinsa Malam Yusuf.
Rundunar ‘yan sandan jihar ita ma ta tabbatar da aikuwar haka wa PREMIUM TIMES ranar Litini.
Majiya a Yandoto mai suna Aliyu Bashar ya ce ‘yan bindigan sun sace Rabi’u a hanyar zuwa Gusau.
“Na samu labarin cewa ‘yan bindigan sun kama Rabi’u a hanyarsa Gusau daga Yantodo.
“Rabi’u ya bar gida tare da ‘ya’yan da biyu saboda yana da mata a gi Gusau inda kafin ya Kai maharan suka kama shi.
Ya ce ya fara jin harbin bindiga da misalin karfe 7:33 na dare daga wajen Yantodo.
Bashar ya ce mahara na yawan garkuwa da mutane musamman a hanyar Tsafe zuwa Gusau.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Mohammed Shehu ya tabbatar da haka ya kuma kara da cewa rundunar ta fara gudanar da bincike domin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.
Discussion about this post