Hukumar EFCC ta bayyana abin da ta kira gagarimar nasarar da ta samu a shekarar 2022, daga Janairu zuwa Disamba, inda ta gurfanar da mutum 3,785 a kotu cikin shekarar wadda ta gabata.
Kakakin Yaɗa Labaran EFCC, Wilson Uwujaren ne ya bayyana haka a ranar Laraba, a Abuja.
Uwujaren ya ce daga cikin waɗanda aka gurfanar ɗin, a shari’u 41 ne kaɗai EFCC ba ta yi nasara ba, amma sauran 3,744 duk ta yi nasara a kotu.
Sai dai kuma Uwujaren a ce rabin waɗanda aka gurfanar ɗin tare da yanke masu hukunci, duk ‘yan damfarar yahoo-yahoo ne.
Kakakin na EFCC, ya ce daga Janairu zuwa Disamba, 2022, hukumar su ta ƙwato naira bilyan 134.33, dalar Amurka miliyan 121.76, fam na Ingila 177, Yen 21,350 da kuma saifa 300,000.
Ya ce a Shiyyar Legas ne aka fi gurfanar da mutane, har 765, sai Ibadan mai 573, Shiyyar Fatakwal kuma 567, sai Abuja 341.
Cikin 2015 dai EFCC ta gurfanar da mutum 103, cikin 2016 kuma mutum 195, a 2018 mutum 312 sai kuma 2019 mutum 1,280.
EFCC ta gurfanar da mutum 976 kotu a cikin 2020. Adadin bai yi yawa ba a shekarar saboda ɓarkewar annobar korona.
Cikin shekarar 2021 kuma EFCC ta gurfanar da mutum 2,220.
Discussion about this post