Bankunan kasuwanci a faɗin ƙasar nan ma ci gaba da yi wa Babban Bankin Najeriya (CBN) gunagunin ƙarancin sabbin kuɗaɗe, duk kuwa da ƙarin kwanaki 10 da aka sanar a ranar Lahadi.
A ɓangaren masu tsoffin kuɗaɗe a hannu da masu kuɗi ajiye a banki kuwa, har yau ba su daina ganin tsoffin kuɗaɗe na fitowa idan sun ciri kuɗi ta P.O.S ba.
PREMIUM TIMES ta kuma tabbatar da matsanancin ƙarancin sabbin kuɗaɗe a hannun masu POS, lamarin da ya kai yawancin su ma duk sun rufe shagunan hada-hadar kuɗaɗen su.
Ƙarancin sabbin kuɗaɗen ya fi shafar ƙananan garuruwa da kuma yankunan karkara.
Fatar da sanarwar yin ƙarin wa’adin kwanaki 10 ke da wuya, sai wasu masu sayar da kayan masarufi da dama a Kano da direbobin Keke NAPEP su ka ci gaba da karɓar tsoffin kuɗaɗe. Amma fa akwai mutane da dama da su ce ƙarin wa’adin ba zai sa su yi dakon wata sabuwar wahala nan da bayan mako ɗaya ba.
Dalili kenan su ka ce su dai ba za su sake mu’amala da tsoffin kuɗaɗen ba.
Majiya daga masu kusanci da halin ko masaniyar halin da CBN ke ciki, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa har yanzu babu wadatattun kuɗaɗen da za su wadaci bankunan kasuwanci, ballantana su raba wa kwastomin su.
Majiya daga sashen tsaro ta shaida wa wannan jarida cewa Naira miliyan 12 kaɗai rassan bankuna ke samu a kullum, adadin da ya yi kaɗan sosai da sosai.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda wannan ƙaƙudubar canjin kuɗi ta kai har wani lauya ya maka CBN kotu, ya na neman a tsawaita lokacin daina karɓar tsoffin kuɗaɗe.
Wani lauya mai suna Joshua Alobo, ya maka Babban Bankin Najeriya (CBN) kotu, inda ya nemi kotu ta soke wa’adin ranar 31 Ga Janairu da CBN ya bayar, a matsayin ranar daina amfani da tsoffin nairori.
Alobo, wanda farfesa ne a fannin lauya da shari’a, ya nemi Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke ranar da CBN ta bayar, wato 31 Ga Janairu a matsayin ranar daina karɓar tsoffin kuɗaɗe.
Kuɗaɗen da CBN ya sauya wa launi dai sun haɗa da takardun naira 1,000, takardun naira 500 da takardun naira 200.
Hususan dai shi mai ƙara ya roƙi kotu ta umarci CBN ya ƙara wa’adin daina amfani da tsoffin kuɗaɗen da aka sauya wa launi zuwa ƙarin makonni uku yadda sabbin takardun nairori.”
Waɗanda lauyan ya maka kotu sun haɗa da CBN, Gwamnan CBN Godwin Emefiele da kuma Antoni Janar na Tarayya, wanda shi ne Ministan Harkokin Shari’a.
Alobo ya aika da kwafen bayanan sa ta hannun lauya Musa Damudi, mai ɗauke da bayanin cewa an ƙaddamar da amfani da sabbin N1,000, N200 da N500 a ranar 26 Oktoba, 2022.
Alobo ya nuna wa kotu damuwar sa ganin yadda masu ƙaramin ƙarfi ke ci gaba da fuskantar matsananciyar wahalar canjar da kuɗaɗen su, saboda ƙarancin sabbin kuɗaɗen a bankuna da kuma hannun masu hada-hadar musayar kuɗaɗe ta tsarin POS.
Ya ce zalunci ne ƙarara da CBN ya bayar da taƙaitaccen lokacin canja kuɗaɗe, alhali har yau bankunan kasuwanci sun ƙi wadatar da sabbin kuɗaɗen ga jama’a.
Ya ce har zuwa ranar 25 Ga Janairu bankuna na ci gaba da bayar da tsoffin kuɗaɗen da za a daina amfani da su.
Ya ce haka lamarin ya ke, idan mutum ya je ATM, maimakon a zubo masa sabbin kuɗaɗen ya kwasa, sai a zubo maka tsoffi, ko da kuwa kai tsoffin ne ka mutum ya kai banki ajiya a ranar.”
Ya ce haka manyan kantinan sayen kayan masarufi da kayan alatu duk sun daina karɓar tsoffin kuɗaɗe, su kuma bankuna ba su bayar da fiye da naira 20,000 a ATM a rana ɗaya.
Ana dai ci gaba da karankatakaliyar neman rabuwa da tsoffin kuɗaɗen da ke hannun mutane, malarin da ya jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin matsananciyar wahala, inda cinikayya ke neman tsayawa cak a faɗin ƙasar nan.