Ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya bayyana cewa goyon bayan da ya ke wa Shugaba Muhammadu Buhari mai ɗorewa ne har bayan da zai sauka daga mulki.
Tinubu ya bayyana haka a Gusau, Babban Birnin Jihar Zamfara.
Ya kuma ƙara da cewa babu wani saɓani tsakanin sa da Shugaban Ƙasa.
Kwanan nan ne dai Tinubu ya ce an ƙirƙiro matsalar wahalar fetur da jalli-jogar canjin kuɗi a wannan lokaci don a taɗiye shi daga yin nasara a zaɓen 2023.
Bai dai bayyana waɗanda ya ke zargin su na bin sa a baya su na yi masa taɗiyar ba, to amma dai an haƙƙaƙe cewa Buhari ya ke nufi, domin shi ne ya amince wa Gwamnan CBN Godwin Emefiele, kuma ya ba shi goyon bayan sauya launin kuɗin a daidai wannan lokaci da ake kusa ga yin zaɓen 2023.
A ranar Juma’a Tinubu ya je Daura domin ganawa da Buhari, ziyarar da ake ganin cewa ya je ne domin ya gamsar da Shugaban Ƙasa fa’idojin da ke tattare da ƙara wa’adin daina karɓar tsoffin kuɗaɗe.
Tinubu ya ce Buhari mutumin kirki ne. Haka ya jaddada a Gusau ranar Asabar, a wurin kamfen ɗin APC a jihar.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Tinubu, Abdul’aziz Abdul’aziz ya fitar, ya ce Tinubu ya yi alƙawarin shawo kan matsalolin tsaron da ke addabar ƙasar nan. Kuma zai bunƙasa noman rani sosai.
“Na goyi bayan Buhari tun ma kafin ya zama shugaban ƙasa. Zan ci gaba da goyon bayan sa, tare da kasancewa abokin sa har bayan ranar da ya kammala wa’adin mulkin sa.”
Discussion about this post