Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Nasarawa ta tabbatar da rahotannin kashe wasu makiyaya 27 a wani harin da aka yi iƙirarin cewa daga jirgin sama aka buɗe masu wuta a Ƙaramar Hukumar Doma.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Nasarawa, Rahman Nansel ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) adadin waɗanda aka kashe ɗin.
Ya yi masu jawabin ne a Lafiya, babban birnin jihar, a ranar Alhamis.
Nansel ya ƙara da cewa makiyayan sun je Jihar Benuwai a ranar Talata domin biyan haraji da kuɗin tarar da Hukumar Hana Kiwo ta Jihar Benuwai ta ƙaƙaba wa wasu shanun su da aka kama a can.
Ya ce yayin da su ke loda shanun na su a cikin manyan motoci a cikin dare a dajin ƙauyen Kwatiri, wanda ke kan iyakar Jihar Benuwai da Nasarawa, sai wani abu mai kama da jirgin yaƙi ko na’urar ‘drone’ ya riske su ya buɗe masu wuta.”
Nansel ya ce Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Nasarawa, Maiyaƙi Mohammed-Bala ya ziyarci wurin da kuma wurin da aka sallaci mamatan.
Mohammed-Baba ya je ne tare da Mataimakin Gwamnan Nasarawa, Emmanuel Akabe da wasu Sarakunan gargajiya.
Ya ce ana ci gaba da binciken masu hannu a kisan, sannan kuma an baza jami’an tsaro a yankin domin hana ɓarkewar rikicin ramuwar-gayya, ko karya doka da oda a yankin.
Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Adamu ya yi Allah-wadai da kisan, kuma ya ce ya na tuntubar takwaran sa na Benuwai a kan lamarin.
Sannan kuma ya ce jami’an tsaro su na kan bincike.
Ya yi kira ga jama’a su kwantar da hankali kada su ɗauki doka a hannun su.
Ita ma Kungiyar Fulani Makiyaya ta Ƙasa, MACBAN, ta yi tir da wannan mummunan kisan gilla. Ta ce tilas a yi ƙwaƙƙwaran bincike, kasancewa wannan ne karo na uku da aka taɓa yi masu haka.
Discussion about this post