Gwamnatin jihar Bauchi ta shiga tsakanin takaddamar filin maƙabarta da ake yi tsakanin musulmai da kiristocin unguwar Yolan Bayara, dake kusa da cikin garin Bauchi.
Shugaban al’ummar yankin Yolan Bayara Sani Yakubu ya zargi gwamnatin jihar da kwace wa musulmai filayen noman su ta baiwa kiristoci su ruka birne gawawwakin su. Sannan kuma gwamnati ba ta maida musu da wani ba.
Yakubu ya ce, ” Adalci kenan gwamnati ta maida mana da wasu filiyen a madadin namu da suka ba kiristoci su yi mƙarbata.
Kakakin gwamnan jihar, Mukhtar Giɗaɗo ya bayyana cewa gwamnati ta shiga cikin maganan gadagadan, yana mai yin ƙarin haske cewa gwamnati ta kafa kwamiti karkashin mataimakin gwamnan jihar Baba Tela, domin ya duba matsalar da kuma korafe korafe da ake yi akan wannan fili.
Giɗaɗo ya ce nan ba da dadewa ba gwamnati za ta fidda rahoto game da binciken da aka yi da kuma matsayar gwamnati akai da ya haɗa da abinda za ta yi akai.