Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Sokoto ta jingine tare da soke hukuncin tsige Dauda Lawal daga takarar gwamnan Zamfara a ƙarƙashin PDP, wanda babbar Kotun Gusau ta yi a baya.
Babbar Kotun Gusau dai ta tsige Dauda Lawal daga takarar gwamnan Zamfara, bayan da ta yanke hukuncin cewa zaɓen da ya kai Lawal ga yin nasarar takarar fidda-gwanin PDP haramtacce ne.
Sai dai kuma a ranar Juma’a ɗin nan ce Mai Shari’a Muhammad Shuaibu da wasu alƙalai biyu na Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Sokoto, su ka yanke hukuncin cewa zaɓen halastacce ne.
Daga nan kuma kotun ta umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta amince da sunan Dauda Lawal a matsayin ɗan takarar PDP a zaɓen gwamnan jihar Zamfara, wanda za a fafata a cikin watan Maris, 2023.
Jim kaɗan bayan yanke hukuncin, Lawal a ta bakin kakakin yaɗa labaran kamfen ɗin sa, ya ce “wannan nasara ba ta shi ba ce shi kaɗai ko shi da PDP. Ya ce nasara ce ga dimokraɗiyya da al’ummar jihar Zamfara baki ɗaya.
Idan ba a manta ba, cikin Satumba ne ɗaya daga cikin masu takarar fidda gwani, wato Honorabul Ibrahim Shehu ya maka Lawal da INEC kotu, inda ya ƙalubalanci sakamakon zaɓen fidda gwanin.
Haka kuma idan ba a manta ba, Gwamna Bello Matawalle ya ci zaɓen 2019 a ɓagas, a ƙarƙashin PDP, amma daga baya ko da ya shiga mulki, sai ya koma APC.