Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya yi wa ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu alkwarin kashi 98% bisa kashi 100% na ilahirin ƙuri’un da za a jefa a jihar a zaɓen 2023.
Kalaman Sanata Lawan kenan su na nufin ba za su bari PDP, NNPP, LP da sauran jam’iyyun adawa su samu komai a Jihar Yobe ba.
Lawan wanda ya yi wannan cika-bakin a ranar Lahadi, ya ce jihar Yobe jihar APC ce, don haka za su yi duk abin da za su yi bakin ƙarfin su domin tabbatar da cewa Tinubu da Kashim Shettima sun yi nasara a zaɓen ranar 25 Ga Fabrairu, 2023.
Ya ce haka a sauran zaɓuka na dukkan matakai tun daga gwamnoni da na majalisun ƙasa da na majalisar jihohi, duk za su samar wa APC nasara a zaɓukan.
Lawan ya yi wannan alwashin yayin da ake ƙaddamar da Rundunar Yaƙin APC ta Jihar Yobe, wanda aka gudanar da Gidan Gwamnatin Jihar Yobe, a garin Damaturu.
Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen dai tsohon Gwamna Ibrahim Geidam ne shugaban ta, sai kuma Ahmed Lawal a matsayin shugaba na biyu. Sai kuma Sanata Bukar Abba, wanda shi ma tsohon Gwamna ne a jihar, shi aka na naɗa uban gayya.
Sanata Lawan wanda a yanzu haka shi ne Shugaban Majalisar Dattawa, ya ce za su yi iyakar ƙoƙarin da za su yi, domin su tabbatar da APC ta samu gagarimar nasara a zaɓe mai zuwa.
“Kamar yadda ku ka sani, mu a Jihar Yobe duk ‘yan gida ɗaya ne a siyasance. Da yardar Allah mu ne za mu fi kowace jiha samar wa APC ƙuri’u a zaɓe mai zuwa.
Discussion about this post