Gwamnonin da ke adawa da takarar Atiku Abubakar sun halarci kamfen ɗin tazarcen Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo da aka ƙaddamar a ranar Alhamis, a Ibadan babban birnin jihar.
Dukkan gwamnonin huɗu sun isa a cikin motar bas mai launin baƙi, inda taron ya samu halartar ɗimbin magoya baya a Mapo Hall.
Gwamna Nyesom Wike na Ribas, Okezie Ikpeazu na Abiya, Samuel Ortom na Benuwai da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu duk sun halarta, tare da mai masaukin baƙi Makinde.
Sai dai kuma Shugaban Jam”iyyar PDP Iyorchia Ayu da Atiku Abubakar ɗan takarar shugaban ƙasa duk ba su halarta ba.
Tsohon gwamnan Ondo Olusegun Mimiko da Ayodele Fayose tsohon Gwamnan Ekiti duk sun halarta. Su biyun sun yi anko iri ɗaya da na Gwamnonin PDP 5 masu kiran kan su G5.
Shi ma Mataimakin Gwamnan Oyo, Bayo Lawan ya halarta, kamar yadda ita ma uwargidan Gwamna Makinde, Tamunominini ta na wurin.
Wutar lantarki ta ɗauke ɗif yayin da fitaccen mawaƙin Yarabawa Saheed Osupa ke tsakiyar cashewa ana rawa. Sai da aka shafe minti 25 kafin a dawo da hasken lantarki a zauren taron.
Cincirindon jama’a ya sa tilas jami’an tsaro su ka rufe dukkan manyan titinan d ake bi a kai ga wurin ƙaddamarwar, wato Mapo Hall.
Wasu da dama sun bayyana cewa masu zagon ƙasa ne su ka yi sanadiyyar ɗaukewar wutar.
Wani mai suna Hakeem Aina ya riƙa magana da Yarabanci ya na cewa, dukkan waɗanda su ka halarci taron sun je ne don su samu kuɗi kawai ba don wani abu ba.
Wasu a wurin sun riƙa nuna goyon bayan su ga Atiku, su na cewa Gwamnonin G5 su na adawa da Atiku don wani muradi na su kawai.
Sai dai kuma kwana ɗaya kafin ƙaddamar da tazarcen Makinde a Oyo, wasu gungun ‘yan PDP sun yi tattaki don nuna goyon bayan Atiku a Ibadan.
Discussion about this post