Jam’iyyar PDP reshen Jihar Katsina ta ƙaryata iƙirarin da APC ta yi cewa ta karɓi mambobin ta har 1,900 daga Ƙaramar Hukumar Ɗanmusa a ranar Lahadi.
Ɗanmusa dai can ne mahaifar tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Mustapha Inuwa, wanda ya fice daga APC ya koma PDP.
Kakakin Yaɗa Labaran Kamfen ɗin APC, Ahmed Abdulƙadir, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa “ɗan takarar gwamnan Katsina na APC ya ƙwace wa tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina mabiyan sa a garin haihuwar sa.”
Sanarwar ta ce a cikin waɗanda su ka sauya sheƙa daga PDP su ka koma APC a Ƙaramar Hukumar Ɗanmusa, har da fitaccen ɗan siyasa Sani Abu, wanda aka fi sani da Minista.
“Ɗan takarar gwamnan Jihar Katsina a APC ya yi wa Ƙaramar Hukumar Ɗanmusa dirar-mikiya, inda ya kwashe magoya bayan tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Mustapha Inuwa.
“Fiye da ‘yan PDP 1900 masu goyon bayan Mustapha Inuwa ne su ka koma APC. Kuma nan take a cikin Ɗanmusa ɗan takarar gwamnan na APC, wato Dikko Raɗɗa ya karɓe su.”
Sanarwar ta ce sanannen ɗan siyasar nan Sani Abu ne ya gayyato su duk su ka koma APC, daga mazaɓu 11 na ƙaramar hukumar.
‘Ƙarya APC Ke Yi, Ina Waɗanda Su Ka Canja Sheƙar?’ – PDP:
A cikin sanarwar da Kakakin PDP na Katsina, Kabir ‘Yar’Adua ya fitar, ya ce zancen APC duk ƙarya ce, kuma ya ƙalubalanci a nuna wa jama’a mutanen da su ka sauya sheƙa ɗin daga PDP su ka koma APC.
Kabir ya ce APC ba wata tsiya ba ce sai “gungun mayaudara, maƙaryatan da su ka ƙware wajen yaɗa labaran bogi.”
Ya ce kowa ya ga yadda APC ta je da sojojin-haya ‘yan jagaliya daga ƙananan hukumomi, su ka ce wai su ne su ka koma APC a Karamar Hukumar Ɗanmusa.
Discussion about this post