Ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar LP, Peter Obi, ye bai kamata a riƙa damƙa shugabancin Najeriya a hannun dattawan da za su riƙa maida fadar shugaban ƙasa wani dakalin zaman cin kuɗin tsoffin ‘yan fansho ba.
Obi ya bayyana haka a ranar Talata, a wurin wani taron ganawa da Majalisar Sarakunan Gargajiyar Jihar Anambra.
An gudanar da taron a garin Awka, babban birnin jihar.
Obi ya bayyana cewa ƙarfin ikon shugaban ƙasa babban muhimmin abu ne, wanda bai kamata ‘yan Najeriya su tafka kuskuren zaɓen baibawan-burmi a matsayin shugaban ƙasa, a ranar 25 Ga Fabrairu ba.
Sai dai Obi bai bayyana abin da ya ke nufi da dattawan zaman dakalin cin kuɗin fanshon masu ritaya ba.
Obi ya ɗora matsalar, tsadar rayuwa, rashin aikin yi da sauran matsaloli a kan damalmalallen tsarin tattalin arziki da ake tafiyar da shi a ƙasar nan.
Ya ce idan Najeriya ta tashi daga ƙasar da ke samar da abin da ta ke ci kawai ba tare da sarrafa kayan da duniya ke buƙata, to za a samu ci gaba.
Daga nan ya bada shawarar Najeriya ta yi amfani da albarkatun arzikin noma domin a magance matsalar rashin aikin yi.
Daga nan ya roƙi Sarakunan Gargajiya su goyi bayan samar da shugabanni nagari.
“Mutum ya zauna tsakiya ba tare da nuna goyon bayan wanda ya dace a zaɓen 2023 ba, to zai zame wa ƙasar babbar matsala ga ƙasar nan.
“Na san cewa dokar ƙasa ta umarci sarakunan gargajiya su ƙaurace wa siyasa. To amma idan su ka riƙa zura idanu ana zaɓen baragurbin shugabanni, to abin su ma zai shafe su.” Inji Obi.