-
Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara, Monica Dongban-men ta gargaɗi rajistarorin da za su yi aiki a Kotunan Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓe cewa, duk wanda aka kama ya karɓi kuɗi a hannun ‘yan takara sai an kore shi daga aiki, sannan kuma a hukunta shi.
Dongban-men ta yi wannan gargaɗin a lokacin sa da yake yin jawabi wurin taron sanin makamar aikin rajista a Kotun Ɗaukaka Ƙara.
An shirya sanin makamar aikin rajista, wanda aka yi a Cibiyar Kula da Harkokin Shari’a (FJSC), a Abuja.
“Kada son abin duniya ya ruɗe ku har wani ɗan ƙadagin ɗan siyasa ya ba ku kuɗi. Hakan idan ku ka karɓa, za ku jefa kan ku cikin ruɗun da zai zubar maku da mutunci kuma ya zubar da ƙimar harkar aikin shari’a da kotu ɗungurugum.
Cikin watan Nuwamba, 2022 ne Babban Jojin Najeriya, Olukayode Ariwoola ya rantsar da alƙalai 300 waɗanda za su yi shari’un jayayyar sakamakon zaɓen 2023 mai zuwa.
A Kotun Ɗaukaka Ƙara dai ne zai kasance Sakateriyar Kotunan Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓe.
Dongban-men ta ce kada rajistarorin su maida aiki a Kotun Ɗaukaka Ƙara ya kasance mafakar da za su zubar da mutuncin su har su kai ga karɓar kuɗaɗe.
Za dai a yi zaɓen Shugaban Ƙasa a ranar 25 Ga Fabrairu, shi na da ‘yan Majalisar Tarayya.
Discussion about this post