Wani magidanci kuma dan kasuwa Justine Onu ya roki kotu a Jikwoyi dake garin Abuja da ta warware kullin aurensa da matarsa Joyce saboda mugun hali irin nata sai da na kamu da hawan jini.
Onu ya ce matar sa ta canja kwatakwata daga yadda ya aure ta, bakin hali da take nuna mun ya yi tsanani, ashe muguwar mata ce.
“ Karuwacin matata ya yi tsanani matuka abin ya kai ga hatta ɗan uwanta tana kwana da shi. Ni na da kai na kamata turmi da taɓarya tana zina da ɗan uwanta a gida na.Yaya za a ce zuciyata ba zata ta buga ba, hawan jini ya kama ni.
Onu ya ce matarsa bata da dabaran yadda za ta iya tafiyar da harkokin cikin gidanta yadda ya kamata a matsayinta na matar aure.
” Matata sam bata iya kula da gida ba. Komai nata a yamutse suke babu kan gado. Sannan kuma ga ɓarnata abinci babu tattali. Duk abinda ka bata za ta kashe su.
“Sannan gashi ko iya kula da ‘ya’yan ta ma ba ta iya ba. Dukundukun zaka rika ganin su.
Sai dai kuma Joyce to musanta duka korafin da mijin ya faɗi a kanta
Alkalin kotun Labaran Gusau ya ce za a ci gaba da shari’ar ranar 9 Faburairu.