Rundunar Ƴan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta tsinci gawar wasu ma’aurata mace a kan kadon su a karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar.
Kakakin rundunar Abdullahi Haruna-Kiyawa ya sanar da haka a garin Kano ranar Laraba.
Ya ce rundunar ta tsinci gawar Sulaiman Idris mai shekara 28 da Maimuna Haliru 20 mace a cikin dakinsu.
“ A ranar 3 ga Janairu da misalin karfe 9 na dare rundunar ta samu labarin wasu ma’aurata sun mutu a kauyen Kwa dake karamar hukumar Dawakin Tofa.
“Ma’auratan tun da suka shiga dakin su suka kwanta da karfe 11 na daren ranar 2 ga Janairu ba su sake fitowa ba har sai bayan wayewar gari.
“Kakan Idris ta ce sai da aka ɓalla kofar dakin sai suka iske ma’auratan a mace hayakin garwashin wuta da suka saka domin su ji dumi ya tirnike ɗakin.
“ Ko da aka kai su asibitin Murtala a Kano, Likitoci sun tabbatar cewa sun mutu cikin barcin su dalilin shaƙar hayakin da suka yi.
Haruna-Kiyawa ya ce binciken da ‘yan sanda suka gudanar ya nuna cewa hayakin garwashin wutan da ma’auratan suka kuna ne ya kashe su.
Ya ce rundunar za ta ci gaba da bincike akai.
Haruna-Kiyawa ya yi kira ga mutane da a maida hankali matuka wajen saka wuta a daki a musamman wannan lokaci da ake buki da iska.
Discussion about this post