‘Yan makarantar firamare da dama sun rasa damar da su ke da ita ta samun ilmi, saboda mutanen da ke cincirindon tserewa daga hare-haren ‘yan ta’addar Boko Haram, sun cika ajujuwan da yaran ke karatu, sun mayar da makarantun sansanonin masu gudun hijira.
A ranar 20 Ga Yuli, 2022 wakilin mu ya je binciken gani-da-ido a sansanin masu gudun hijira da ke Kuta a Jihar Neja. A wurin ya ga dandazon mutane wasu mazaje zaune kan rugurguzajjen bangon da ya kewayen makarantar. Can gefe kuma ga wasu mutanen zaune su na taɗi a ƙarƙashin inuwar kuka, sun ƙura wa wakilin mu idanu, su na kallon-kallo.
A wani gefen kuma ga mata can zazzaune, waɗansun su da dama ɗauke da goyon ƙananan yara, wasu na rungume da jarirai sun jingida da bango a sansanin.
Idan ka na zagayawa idanun ka su ka kai cikin ajujuwan ɗalibai da aka mayar makwancin masu gudun hijira, babu komai sai tarkacen tukwane, kwanuka da farantai, yarbatsulan tufafi da tsummokara, bokitan robobi da kwanukan roba.
A waje kuma an shashshanya zannuwa, fatari da kayan ƙananan yara waɗanda ba su kai ga bushewa ba. Sannan ko ta ina ga kwanyamin yara nan wasu na wasa, wasu na sagarabtu, wasu kuma na ƙiriniyar da yaran da ba su da mai ce masu yi, ko ku bari ke yi.
A makarantar akwai aƙalla masu gudun hijira 2,500, cikin wannan makarantar firamare ta garin Kuta, inda masu gudun hijirar da ke zaman-dirshana ajujuwa da kewayen makarantar su ka haddasa tsaida koyar da yara darussan ilmi a tilas.
Lokacin da PREMIUM TIMES ta kai ziyara makarantar wadda a yanzu ta zama sansanin masu gudun hijira, babu wata alamar da ke nuna cewa mazauna cikin ajujuwan za su fice nan kusa, saboda su ma gudun ceton rayukan su su ka yi, kuma gwamnati ba ta ce masu ga mafita ba.
A ranar da wakilin mu ya je, sai can wajen ƙarfe 10 na safe ya fara ganin ɗaiɗaikun ‘yan firamare sanye da yagalgalallun kayan makaranta su na rara-gefe a harabar makarantar. Su ba wurin zama su yi karatu gare su ba, sannan kuma riga-malam-masallaci su ka yi, domin babu malami ko ɗaya da ya je makarantar.
Yayin da ‘yan bindiga da ‘yan Boko Haram su ka fitini ƙauyukan cikin yankunan karkara, dubban jama’a sun gudu zuwa cikin garuruwan da su ke ganin tudun-mun-tsira ne, ciki kuwa har da garin Kuta, inda su ka yi kaka-gida a Kuta Central Primary School.
Sai dai kuma takaici goma da ashirin kenan. Can ‘yan Boko Haram sun hana su ci gaba da rayuwa a yankunan karkarar da su ka gudo. A cikin gari kuma sun hana yara ‘yan makaranta ci gaba da karatu, saboda sun yi mamayar kaka-gida a cikin ajujuwan su.
Mutane da yawa da wakilin mu ya tattauna da su a Kuta, sun ce sun hana yaran su zuwa makarantar, wasu ma sun cire ‘ya’yan su, saboda karatun ya tsaya cak, sanadiyyar masu gudun hijira sun mamaye makarantar.
Irin yadda masu gudun hijira su ka yi wa Makarantar Firamare ta Kuta, haka su ka yi wa ta garin Gwada, gari wanda cikin minti 20 za ka iya tashi ka isa Minna, babban birnin Jihar Neja. A Gwada kwata-kwata an ma daina batun karatun, ba kamar Kuta inda wasu lokuta a kan ɗan taɓa kaɗan a waje.
Yawancin masu gudun hijira ɗin nan, sun tsere ne daga ƙauyukan Kawure da ke yankin Shiroro da ƙauyukan da ke kewaye da garin. An hana masu rayuwar su ta noma, kuma an hana yaran su zuwa makaranta. Su kuma sun gudo sun hana yaran da ke mafakar su ci gaba da na su karatun.
A makarantar firamare ta Kabir Erena inda ke da ajujuwa 20, majiya ta ce, “an raba ajujuwan ne inda masu gudun hijira ke cikin rabi. Rabin kuma ɗalibai na karatu, amma a yanzu hutu su ke yi.”
Dukkan sansanonin gudun hijirar da wakilin mu ya je, waɗanda makarantun firamare ne, kukan su iri ɗaya ne, wato ‘yan ta’adda sun kore su daga yankunan su, sun kashe na kashewa, kuma an hana su yin noma da sana’o’in su. Sannan wani abin takaicin shi ne “yadda gwamnati ta yi watsi da mu.”
Haka nan kuma babban babun da ta fi damuwar mazauna sansanonin ita ce babun abinci. Wakilin mu ya lura ana fama da rashin abinci sosai da kuma rashin kula da lafiya a matakin farko.