Yayin da ake ƙasa da kwanaki 30 a gudanar da zaɓen 2023, wasu ƙungiyoyin kare dimokraɗiyya su 10 sun fito da rahoton da ke nuna yiwuwar yi wa zaɓen 2023 kancal a wasu jihohi 22, daga cikin jihohi 36 da ke ƙasar nan.
Rahoton mai ɗauke da bayanin har shafuka 26, sun fitar da shi ne a ranar Juma’a.
Rahoton dai wata ‘yar manuniya ce da ƙungiyoyin 10 su ka fitar, domin a gaggauta ɗaukar matakan hana kawo wa zaɓen na 2023 cikas a jihohin.
Ƙungiyoyin 10 sun haɗa da Yiaga Africa, CJID, SBM Intelligence, Dataphye, IPC, IMS, PER, The Albino Foundation, The Kukah Foundation da kuma Enough is Enough for Nigeria.
Masu binciken sun ce nazari da binciken su ya dogara ne bisa bibiyar ababen da su ka riƙa wakana a baya, tattaunawa da masana da ƙwararru.
Bayanan da su ka tattara daga waɗannan hanyoyi ne su ka bayar da hasashen cewa akwai yiwuwar ‘yan fancale su yi wa zaɓen 2023 kancal a waɗannan jihohi 22.
Rahoton ya kasa jihohin 22 zuwa gida uku: Akwai Ƙwaƙƙwaran Hasashe, Tsaka-tsakiyar Hasashe da kuma Rasashe Mai Rauni.
Hasashe Mai Ƙarfi:
Jihohi 22 ɗin sun haɗa da Imo, Anambra, Enugu, Ebonyi, Abia, Rivers, Akwa-Ibom, Legas, Oyo, Osun, Ekiti, Kwara, Neja, Filato, Taraba, Kaduna, Bauchi, Adamawa, Kano, Katsina, Sokoto da Jigawa.
Hasashe Tsaka-tsakiya:
Akwai jihohi 12 da rahoton ya yi wa hasashe tsaka-tsakiya. Sun haɗa da Barno, Yobe, Nassarawa, Benue, Kogi, Zamfara, Kebbi, Ogun, Edo, Delta, Bayelsa da Cross River.
Jihohi 3 Masu Hasashe Mai Rauni: Su ne jihohin Gombe, Ondo da Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja.
Rahoton ya ce a yanzu haka akwai masu ƙoƙarin ganin sun kawo wa zaɓen 2023 cikas.
Yi Wa Zaɓe Kancal:
“Yi wa zaɓe kamcal wata haramtacciyar hanya ce da manyan ‘yan siyasa ke amfani da manya da ƙananan ‘yan jagaliya wajen hana zaɓe ya yi tasiri, ko kuma sa baki a yi ba daidai ba a lokacin zaɓe, musamman ta hanyar amfani da ƙarfin iko ko kuɗi ko wasu haramtattun dabaru.
“Hanya ce ta amfani a ƙarfi, rikici ko kuɗi a sauya sakamakon zaɓe, domin a bai wa wanda ba shi aka zaɓa na nasara.”
Discussion about this post