Tsohon shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya yi kira ga matasa da su fito kwansu da kwarkwata su mara wa dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi baya, yayi shugabancin Najeriya.
A wata doguwar wasika da ya rubuta ranar Lahadi, Obasanjo ya ce lokaci yayi da mata sa za su fito su zabi mutum mai karancin shekaru, kwararre mai kishin kasa a 2023.
Obasanjo ya ce ” Tun ina da shekaru 39 da 42 na zama shugaban kasa, sannan da na kai shekaru 62, na dawa a siyasa, a lokacin da na kai shekara 70 na gama komai. Haka shima Yakubu Gowon, yana da shekaru 30 ya zama shugana kasa. Yanzu dama ce ga matasa su fito su yaki tsoffin nan dsake takara.
” Na san Peter Obi kuma nasan mutum ne mai kwazo da hangen nesa, sannan yana da kwarewa a harkar shugabanci. Dalibi mai kokarin gaske. Ina tabbatar muku ba zai ba mu kunya ba.
” Ina kira ga matasa su daina jijjibar fadar da ba nasu ba. Gaba da kyashin da iyayen su suka yi da wasu, ba nasu bane yanzu. Su watsar da wannan hali su rungumi kowa da kowa a matsayin na su. Abinda ya faru a baya ya wuce, su dai na gaba da juna, a zauna kasa daya dunkulalliya.
Babu wani yanki a kasar nan da zai ce shi shafaffe da mai ne bashi da matsala, kowa na da nashi guntun kashin a baya, sanoda haka mu hakura da juna mu yi abin da ya dace.
” Mata sa ku fito ku nuna karfin ku da kuke da shi.
Discussion about this post