Komandan rundunar Sibul Difens reshen jihar jihar Kaduna Idris Adah ya jajanta wa mutane da iyalan jami’an hukumar da ‘yan bindiga suka kashe a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar DSC Habeeb Badamasi ya sanar da haka a garin Kaduna a lokacin da suka ziyarci iyalan.
Badamasi ya ce ‘yan bindiga sun kashe jami’an hukumar guda bakwai da wasu guda biyar a karamar hukumar Birnin Gwari ranar Litini da safe.
Badamasi ya ce an yi jana’izan daya daga cikin jami’an hukumar da aka kashe ASC1 Shamsudeen Labaran bisa ga sharuddan adinin Musulunci ranar 10 ga Janairu a Anguwan Dosa sannan hukumar ta aika da gawan ASCll Augustine Simon zuwa jihar Benuwai domin yi masa jana’iza.
Haka kuma sauran mutum hudu an yi jana’izan su ranar Asabar.
Adah ya yaba jaruntar ma’aikatan musamman yadda suka gamu da ajalinsu yayin da suke aikin su na kare rayuka mutane.
Ya aika da sakon sa na ta’aziya ga iyalai, ma’aikatan hukumar da sauran mutane.