Ɗan takarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin APC, Bola Tinubu, ya bugi ƙirji da tutiyar cewa shi ne ya ceto Atiku Abubakar ɗan takarar PDP daga hannun Obasanjo a lokacin da tsohon Shugaban Kasar ya nemi babbake tsohon Mataikakin na sa, lokacin su na kan mulki.
Atiku Abubakar wanda shi ma yanzu haka ya ke takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin PDP, ya yi mataimakin Obasanjo daga 1999 zuwa 2007.
Dangantaka tsakanin Obasanjo da Atiku ta yi tsami tsakanin 2003 zuwa 2007, lokacin da Atiku ya nuna sha’awar zama shugaban ƙasa.
Yayin da Tinubu ke wa jama’a jawabi a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom, Jagaban ya ce, “Ni na yi gaggawar ceto Atiku daga cikin wutar da Obasanjo ya nemi babbake shi a ciki kamar yadda ake babbake akuya.”
Ya ce aniyar Atiku ita ce ya sayar da Najeriya, ya kwashi la’ada sannan ya gudu zuwa Dubai ya yi zaman sa a can.
Ya yi alƙawarin idan ya zama shugaban ƙasa, zai kammala aikin Tashar Jiragen Ruwa ta Ibom, mai zurfin gaske.
Kuma ya yi alƙawarin kawo ƙarshen rashin aiki yi a ƙasar nan, ta hanyar mayar da ita ƙasaitacciya. Kuma ya ce zai kawo ƙarshen gagarimar matsalar tsaro wadda ita ce ta fi damun mutane a ƙasar nan.
Discussion about this post