Asiya Ganduje diyar Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ta bayyana a kotun shari’a dake jihar Kano cewa za ta dawo da naira 50,000 kudin sadakin da mijinta Inuwa Uba ya biya a kanta domin a raba auren su na shekara 16.
Asiya ta roki kotu ta raba auren ta hanyar ‘Khul’I’ saboda ta gaji da auren Uba.
Lauyan da ya shigar da karar a madadin Asiya, Ibrahim Aliyu-Nassarawa ya ce Asiya a shirye take ta biya Uba naira 50,000 kudin sadakin da ya biya a kanta domin ya sake ta.
“ Duk macen dake dakin ta na aure da bata Jin dadin zama tare da mijinta na da ikon raba auren idan har ta biya kudin sadakin da aka biya a kanta lokacin aure.
“ Asiya a shirye take ta biya Uba sadakin da ya biya a lokacin da suka yi aure.
Aliyu-Nassarawa ya ce Asiya ba ta gaji da zaman auren sannan ba za ta iya ci gaba da yi wa Uba biyayya a gidan aure ba.
Lauyan wanda ake kara Umar I. Umar ya ce batun ya wuce Asiya ta biya Naira 50,000 kudin sadakin da Uba ya biya a kanta.
“Uba ya gindaya wa Asiya wasu sharudda biyu kafin a zo maganar mayar da sadaki ko saki.
“ Asiya da Uba sun haifi ‘ya’ya hudu tare sannan duk kokarin da aka yi domin sasanta su ya ci tura.
“ Ya kamata Asiya ta mayar wa Uba duk takardunsa na gidaje da motocin dake hannun ta sannan ta sadaukar da kasonta na Kamfanin shinkafar da suka gina tare.
Alkalin kotun Halliru Abdullahi bayan ya saurari bayanan bangarorin ya dage shari’a zuwa ranar 2 ga Fabrairu.
Discussion about this post