Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yayi kokarin sa a matsayin shugaban kasan Najeriya.
” Ni fa da kuke gani na yi abinda ya kamata a yi wa ‘yan Najeriya kuma ni na tabbata ban baku kunya ba sai dai ma burge ‘yan Najeriya da nayi a tsawon mulki na.
Shugaba Buhari ya fadi haka ne a lokacin da yake jawabi a fadar sarkin Bauchi a lokacin ziyara da ya kai masa.
Sarkin Bauchi mai martaba Rilwan Adamu ya yabawa shugaba Buhari bisa gyara fasalin zabe da yayi a kasar nan sannan kuma ya gode masa da ya ke ci gaba da aiki da shugaban hukumar Zabe, Yakubu Mahmood, wanda dan asalin jihar ne.
Bayan ziyarar sai shugaba Buhari da tawagar sa suka dunguma filin wasa na Tafawa Balewa domin halartar gangamin kamfen din yan takarar shugaban Kasa Bola Tinubu da Sadique Abubakar wanda shine dan takarar gwamnan jihar a APC.
Discussion about this post