Kakakin Yaɗa Labaran Kamfen ɗin Atiku Abubakar 2023, Daniel Bwala, ya bayyana cewa Obasanjo ya goyi bayan takarar Peter Obi ne saboda kawai ya fake da shi ne ya biya ɓoyayyar manufar sa ta yin zango na uku, wato ‘third term’ lulluɓe da bargon Obi.
A ranar 1 Ga Janairu, 2023 ne dai Obasanjo ya fitar da wasiƙa ga ‘yan Najeriya, inda ya bayyana goyon bayan sa ga takarar Peter Obi na jam’iyyar LP, a zaɓen da za a yi ranar 25 Ga Fabrairu, 2023.
A cikin wasiƙar Obasanjo ya ce kakaf a cikin ɗan takarar babu cikakken nagari. “Amma mai dama-dama a cikin su wanda ya fi sauran cancanta, shi ne Peter Obi.”
Sai dai kuma Bwala ya dira kan Obasanjo, inda ya ce duk wani shugaban da aka yi bayan Obasanjo, babu wanda Obasanjo ɗin bai dira ta kan sa ba, saboda shi a tunanin sa, babu wani da ya yi aikin da ya yi.
“Cikin 2014 ko 2015 ya ragargaji Goodluck Jonathan. Ya zarge shi ya ɗauko sojojin haya ya na horas da su don su kashe wasu ‘yan Najeriya. Cikin 2018 ya zargi Buhari na so ya haddasa tarwatsewar Najeriya.”
Bwala ya ce ‘yan Najeriya ne za su tabbatar da wanda su ke so a zaɓen 2023, ba wasiƙar da wani ya rubuta ya na goyon bayan wani ɗan takarar da idan ya hau mulki ya maida shi yaron sa ba.”
Bwala ya ƙalubalanci Obasanjo da ya riƙa bin Peter Obi wurin kamfen da wurin tarukan ganawa da ƙwararru, idan har da gaske ya ke yi, domin ya ga idan Obi na da farin jini a faɗin ƙasar nan, ko ba shi da shi.