Uwargidan dan takarar Shugaban kasa na jami’yyar PDP Titi Atiku Abubakar ta kalubalanci yan takarar shugaban kasa dukkan su cewa mijin ta shi kadai, Atiku Abubakar na PDP ne ke da lakanin kawao karshen matsalolin Najeriya idan ya zama shugaban kasa.
Titi ta fadi haka ne a wurin taron kungiyar mata na kamfen din dan takaran Shugaban kasa ta jami’yyar PDP na shiyar Kudu maso Yamma da aka yi a Ibadan a farkon wannan makon.
Ta yi kira ga mata da su zabi mijinta Atiku a zabe mai zuwa domin ta sama bayarbiya ta farko da za ta zama Uwar gidan Shugaban kasa.
“ Idan kuka zabi mijina matsalolin halin rayuwar da matsalolin kasar nan za su warware saboda mijina ne kadai ya san matakai da dakarun da zai nada mukamai domin gyara kasan.
Titi ta kara tabbatar da cewa mijinta ba zai bai wa mutane kunya ba idan har ya zama Shugaban kasa.
Bayan haka Shugaban kungiyar mata na kamfen din Modupeola Adeleke-Sanni ta yi kira ga mutane da su gaggauta zuwa ofishin hukumar INEC domin su karbi katin zaben su.
A karshe ta yi kira ga mutane da su zabi ‘yan takara na jam’iyyar PDP a zaben da za a yi ranar 25 ga Fabrairu da 12 ga Maris 2023.