Wata matar aure Sadiya Salihu dake zama a Abuja ta roki babban kotun Gwagwalada ta raba auren ta da mijin ta Mohammed saboda rashin nuna soyayya da kula.
Sadiya ta bayyana a kotun cewa ta auri mijinta Muhammed ranar 17 ga Disamba 2022.
Ta ce sai dai bayan an yi kwanaki da auren sai ta lura da wasu halayyarsa da bata yarda da su ba.
“Kwatsam muna zaune sai Muhammad ya ce na tattara kaya na zai maida ni gidan yayata a Gwagwalada.
“Jin haka sai na kira ‘yan uwana suka zo muka koma gida tare da su.
“ Yayin da nake zama a gida sai Muhammed ya kira ni a waya cewa lalle in zo na kwashe sauran kaya na daga gidan sa.
Sadiya ta ce a dalilin haka ya sa take so a raba auren.
A bayanin da ya yi Muhammed ya ce Sadiya ba ta ba shi hadin kai wajen jima’I ba ta kaurace masa baya samun yadda yake so da ita, shine ya sa yake so a raba auren.
Alkalin kotun Malam Abdullahi Abdulkarim ya hori ma’auratan da su nemi hanyar sassanta kansu.
Abdulkarim ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 14 ga Fabrairu.
Discussion about this post