Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, ya fito a karon farko ya ce kwata-kwata bai taɓa nema ko roƙon ko yunƙurin yin tazarcen ‘third term’, wato zango na uku a 2007 ba.
Ya ce da ya ga dama ko ya na da niyyar yin haka ɗin da ake a lokacin, to ya san loga da tuggu da gidogar da zai kitsa ya zarce ɗin.
Haka nan kuma ya ce “duk da ina goyon bayan Peter Obi, ba zan shiga rundunar yaƙin neman zaɓen sa ba.”
Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa duk da ya na goyon bayan Peter Obi na LP ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2023, ba zai shiga cikin rundunar kamfen ɗin yaƙin neman zaɓen sa ba.
A ranar Alhamis ce ya ce ba zai taya shi zaɓe ba, amma na yi amfani da ɗimbin hikima da darussan da na koya ina ɗora al’amurra bisa turbar da ta dace.
“Ni fa ba na goyon bayan kowace jam’iyyya. Kuma ba zan taya kowane ɗan takara kamfen ba. Na dai bayyana ra’ayi na ne, na faɗi wanda na ke ganin shi ne mafi alheri ga Najeriya.”
Discussion about this post