Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya sake ƙaurace wa gayyatar da Majalisar Wakilai ta yi masa, duk kuwa da barazanar kama shi da Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ya yi.
Majalisar Tarayya na neman Emefiele ne domin ya yi bayanin ƙaƙudubar da ke tattare da jidalin canjin kuɗi, bayan ya ce shi ba zai ƙara wa ‘yan Najeriya wa’adi ko na minti ɗaya daya ranar 31 Ga Janairu, 2023 ba.
A ranar Alhamis Shugaban Kwamiti Ado Doguwa ya yi tir da Emefiele, saboda ya ƙi bayyana, kuma CBN bai turo wakilai ba.
Emefiele ya ce ya ƙi zuwa ne, saboda ba ya ƙasar.
Sai dai kuma Doguwa ya ce, “Emefiele ƙarya ya ke yi. Saboda kowa ya san Emefiele ya dawo ƙasar nan kwanan baya.”
Rigimar ‘Yan Najeriya, Majalisar Tarayya Su Da Gwamnan CBN, Emefiele:
Ƙaƙudubar Canjin Kuɗi: Kakakin Majalisa Gbajabiamila, ya yi barazanar bada sammacin kamo Emefiele, ‘limamin’ canjin sabbin kuɗi
Kakakin Majalisar Tarayya Femi Gbajabiamila ya yi barazanar kama Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele.
Ya ce ba zai tsaya ɓata lokaci ba wajen umartar Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Usman Baba ya buga sammacin kamo Emefiele cikin gaggawa.
Gbajabiamila ya yi wannan barazanar ce bayan ya karɓi rahoton kwamitin Honarabul Ado Doguwa, wanda aka ɗora wa nauyin ganawa da Kwamitin Lura da Bankuna da kuma Babban Bankin Najeriya, CBN.
Doguwa ya ce CBN da Emefiele sun ƙi amsa gayyatar bayyana a gaban kwamitin majalisar tarayya a ranar Laraba.
“Kwamitin mu ya gayyaci CBN a ranar Laraba, juya kenan, mu ka ce ya zo shi da manyan jami’an bankin. Amma ina faɗi da babbar murya a cikin tsananin damuwa da takaici cewa CBN da Emefiele sun baɗa mana ƙasa a ido, sun ƙi zuwa.
“Gwamnan CBN bai zo ba, kuma CBN ɗin bai aiko wakilai ki wakili ko ɗaya ba.”
Daga jin haka, sai Gbajabiamila ya ce a shirye ya ke ya yi amfani da Sashe na 89(1)(d) na Dokar 1999, wanda ya bai wa Majalisa ƙarfin ikon umartar jami’an tsaro su kamo mata duk wanda doka ta bada damar a kamo.
Wannan lamari dai ya zo ne daidai lokacin da ake kuka da matsalar canjin sabbin kuɗi, waɗanda Emefiele ya ce ba za a ƙara ko awa ɗaya daga ranar 31 Ga Janairu ba, ranar da za a daina amfani da tsoffin kuɗaɗe.
‘Yan Najeriya na ci gaba da shiga cikin jangwangwamar canjin kuɗi a bankuna, saboda ƙarancin sabbin kuɗaɗen a jihohi da dama.
Abin ya yi munin da har wasu na barazanar shiga fashi da makami ko satar kadarorin gwamnati idan har su ka yi asarar kuɗaɗen su.