Kotun majistare dake Sabo-Yaba a jihar Legas ta gurfanar da wata mata mai gidan haya Temitope Olayiwola mai shekara 45 bayan ta yaye kwanon dakin wasu dake zaman haya a gidanta.
Kotun ta tsare Olayiwola dake zama a Plot 15 rukunin gidajen Oyadiran a Sabo-Yaba bisa laifukan da suka hada da lalata gidan da mutane ke ciki da gangar sannan da tada hankalin jama’a.
Dan sandan da ya shigar da karar Thomas Nurudeen ya ce Olayiwola ta aikata wadannan laifuka ne ranar 10 ga Disambar 2022.
Nurudeen ya ce a wannan ranar Olayiwola ta cire kwanon dakin da Edem Yves da Evans Anyanwu ke zama ciki.
Ya ce ta yi haka ne saboda kin biyan kudin hayan da Yves da Anyanwu suka yi.
Alkalin kotun Peter Nwak ya Bada belin Olayiwola akan Naira 600,000 tare da gabatar da shaidu uku.
Nwaka ya ce Ayiwola za ta gabatar da shaidun dake zama a wurin da kotun ke da iko akai, ta tabbatar cewa shaidun na aiki kuma suna biyan harajin gwamanati.
Alkalin ya ce za a ci gaba da shari’ar ranar 13 ga Fabrairu.
Discussion about this post