Shugaban Jam’iyyar NNPP na jihar Barno Mohammed Mustapha ya jawo hankalin gwamnan jihar Barno Babagana Zulum kan yadda magoya bayan APC ke yagalgala fastocin ‘yan takarar jam’iyyar a Jihar.
A wata sanarwa wanda Mustapha ya fitar ranar Litinin, ya koka kan yadda yan APC a jihar ke cin mutuncin jam’iyyar a jihar.
Shugaban ya ce a baya-bayan nan an lalata fastoci da dama wadanda suka maida bayan an lalata su a baya. Jam’iyyar ta kashe makudan kudade wajen sake allunan tallace jam’iyyar da ‘yan takarar ta 16 da aka lalata a baya.
“Abin takaici ne da rainin wayau ganin cewa ‘yan jam’iyyar APC da ‘yan barandanta ba wai kawai lalata allunan tallanmukawai suke yi ba, bayan sun lalata sai kuma su maye gurbin na mu da suka yagalgala da na wasu ‘yan takararsu na APC duk da cewa mun biya gwamnatin jihar Borno kuɗin harajin saka wadannan hotuna.
Mutapha ya kara da cewa su a jam’iyyar NNPP, za su ci gaba da bin doka da oda, amma kuma fa an kaisu makura. Ba za su saka ido su bari ana ci musu mutunci a jihar ba sannan gwamnati bata yi komai a kai ba.
” A ganina gwamnati irin na kwararren Farfesa wato Zulum bai kamata ace ita ce ke ruruta wutar tashin hankali da muzgunawa wasu jam’iyyu ba.
Discussion about this post