Gwamnan Babban bankin Kasa, CBN, Godwin Emefiele ya umarci bankunan kasar nan su gaggauta zuwa rassan babban bankin da ke kusa da su su karɓi sabbin takardun naira domin mutane su samu.
Emefiele ya yi wannan kira ne a lokacin da ya ziyarci babbar kasuwar siyar da na’ura mai ƙwaƙwalwa, wato Alƙaryar Komfuta dake Ikeja.
Ya kara da cewa ya fita rangadi ne sa kansa domin gani wa idon sa yadda mutane suka amshi wannan sabbin takardun kudi da kuma wadatuwar sa.
Sai dai kuma ya lura cewa har yanzu akwai ƙarancin yalwatar takardun kuɗin a hannun mutane.
A dalilin haka ya yi kira ga bankuna su garzaya rassan babban bankin kasa a faɗin kasar na su karɓi kuɗin domin sakawa a ARM mutane su iya samu a duk lokacin da suka buƙaci haka.
” Sabbin takardun kuɗin na rassan babban bankin kasa jibge ana jiran bankuna su zo su karɓa amma har yanzu wasu bankunan na biyan mutane da tsoffin kuɗi kuma mun hana haka.
” Saboda a samu wadaruwar kuɗin mu janye wasu dokoki da muka saka ga bankuna kafin su iya samun takardun kudin domin ya wadata cikin ƙanƙanin lokaci.
Babban Darekta a babban bankin Kofo Salam-Alada,ne ya wakilci Emefiele a wannan ziyarar inda ya kara da cewa CBN na kokarin gani wannan kuɗi ya kai ga mutanen Najeriya a ko-ina suka a fadin kasar nan.
Discussion about this post