Kotun dake sauraren kararrakin zaɓe na jihar Osun ta soke zaɓen gwamna Ademola Adeleke na jihar.
Alkalin kotun Terste Kume wanda ya yanke hukunci ya ce an tafka aringizon kuri’u a mazaɓu sama da 700 wanda da sune a ka yi wa Gbenga Oyetola murɗiya a zaɓen
Alkali Kume ya ce idan aka cire waɗannan kuriu to sauran za su nuna Oyetola ne ya lashe zaɓen.
” Bayan tantance yawan kuri’un da aka jefa a zaɓen gwamna, an gano wasu rumfuna sama da 700 da aka tafka maguɗi a waɗannan wurare. Bayan an zame waɗannan kuri’u da ake zargin ba kurin kwarai bane Oyetola na APC ne yayi nasara a zaɓen.
” Saboda haka na yanke hukuncin umartar hukumar Zabe ta gaggauta mika wa hukumar Oyetola na APC shaidar cin zaɓe.
Idan ba a manta ba Adeleke na PDP ne hukunar zaɓe ta bayyana shi da yin nasara a zaɓen gwamna na Osun.
Adeleke ya yi nasara da kuri’u sama da 400,000 inda shi kuma Oyetola ya samu Kuri’u 300,000 da ƴan kai.
Zuwa yanzu Adeleke bai ce komai ba tukunna game da wannan hukunci, sai da kuma yana da damar ɗaukaka kara a kotunan ɗaukaka kara da kotun koli idan bai gamsu ba.
Discussion about this post