A ranar Laraba ne wata babbar kotun majistare da ke Gyadi- Gyadi a Kano, ta bayar da umarnin tsare wasu alkalan kotunan Shari’a su uku, da wasu ma’aikatan kotun 12 bisa zargin satar naira miliyan 500.
An gurfanar da Wadanda ake tuhuma da gaban alkalin kotun, Mustapha Datti, bisa tuhume-tuhume hudu da suka hada da hada baki, cin amanar jama’a, da kuma sata.
Sai dai alkalin kotun bai bayyana sunayen wadanda ake tuhumar ba.
Laifukan sun sabawa sashe na 97, 79, 315, da 289 na dokar hukunta manyan laifuka ta jihar Kano.
Jami’an kotun da ake zargi Sun hada da ma’aikatan ofishin rajistar kotuna, kudi, wasu ma’aikata, da wasu daga waje da ka hada baki da su.
Da yake gabatar da wadanda ake zargin a gaban kotu a ranar Laraba, lauyan masu shigar da kara, Zaharaddeen Hamisu ya shaida wa kotun cewa ma’aikatan shari’a sun yi jabun takardun kotun shari’ar Musulunci da kuma sa hannun wadanda ake tuhuma biyu a bankin Stanbic IBTC inda suka fitar da N484,067,327:07 ta hanyar zamba.
Lauyan mai gabatar da kara ya kuma shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin zamba ta hanyar yin laifi wajen taimakawa wajen fitar da N96,250,000.00 daga asusun fansho na jihar Kano zuwa asusun kotun shari’a, daga bisani kuma ya zura adadin kudin a wasu asusu na sirri daban-daban da ba a san da su ba.
Wadanda ake zargin sun kirkiro takardun tabbatar da mutuwar ma’aikatan gwamnati 15 na bogi kuma sun yi zamba tare da karbar kudaden da hukumar fansho ta samu, kamar yadda mai gabatar da kara ya shaida wa kotun.
Dukkan wadanda ake tuhumar dai sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su, kuma lauyoyinsu sun nemi a ba su belinsu.
Discussion about this post