Kotun majistare dake Ile-Ife jihar Osun ta bada belin Michael Obeyagbor mai shekara 45 kan Naira 500,000 bisa laifin sace aladu 12.
Alkalin kotun A.O. Famuyide ya ce Obeyagbor zai gabatar da shaidu biyu da za su rantse a kotu cewa suna da aikin da suke karbar albashi kuma mazauna wurin da kotun take da iko da shi.
A lisafe dai farashin kudin aladun da Obeyagbor ya sata sun kai naira miliyan 1.2
Dan sandan da ya shigar da karar Emmanuel Abdullahi ya ce Obeyagbor ya saci wadannan aladu ranar 25 ga Disamba da misalin karfe 4:30 na safe a Oniyanrin Mosan dake Ile-Ife.
Abdullahi ya ce Ojo ya bayyana wa rundunar cewa dama Obeyagbor ya kan sace masa dabbobi idan suka fita kiwo.
“Ya ce a wannan rana Obeyagbor ya shigo filin da ya kebe domin kiwon aladun sa dauke da makami, ya tsorata ojo daya kwashe aladu 12.
Ya ce rundunar ta kama Obeyagbor bisa laifukan da suka hada da tada hankalin mutane, sata, kashe daban da ba na sa ba da shiga filin wani ba tare da izini ba.
Daga nan lauyan dake kare Obeyagbor, Gbenga Omiwole ya roki alfarmar kotun ta bada belin Obeyagbor sannan ya tabbatar cewa Obeyagbor zai cika duk sharuddan da kotun za ta bada.
Za a ci gaba da shari’a ranar 16 ga Janairun 2023.
Discussion about this post