Dan takarar shugaban kasa na APC Bola Tinubu ya yi kira ga ‘yan Kabilar Igbo da su yi wa kan su karatun ta natsu su tun da wuri su zabi shi shugaban kasa a zabe mai su.
Hakan na kunshe ne a jawabin da dan takaran yayi a wurin gangamin kamfen da jam’iyyar sa ta APC ta yi a garin Umuahia, Jihar Abia.
A wurin taron Tinubu ya ce abinda yan kabilar Igbo zasu yi wa kan su shi ne su zabe ni shugaban kasa, su zabi ‘yan APC yan majalisun tarayya da majalisar Dattawa.
” Ni fa shawara nake baku Inyamirai, ku yi karatun ta natsu tun da wuri ku zabe ni shugaban kasa, idan ba haka ba kuwa toh za ku ga ana harkokin a kasa ba tare da ku ba. Ni ne lasisin ku na samun abinda da kuke so.
” Sai fa idan ka shuka abu ne zaka yi girbi, idan baka shuka komai ba babu abinda zaka girba sai dai kaga wasu na jin dadi kai ko kana gefe ba ka isa ka zo kusa ba. ”
Tinubu ya fadi haka a garin Enugu a lokacin Kamfen kafin su dunguma garin Umuahia.
Peter Obi ne dan takaran da ya da ya fi yin tasiri a yankin ‘yan kabilar Igbo, sai dai kuma wasu na ganin ba shi da karfin iya kada sauran yan takaran a wasu yankunan kasar. Wasu na ganin harda yankin Kudu maso gabas din.
Discussion about this post