Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta kama wasu mutane 14 da ake zargi da hannu a kisar hakimin Lambata dake karamar hukumar Gawun Babangida a jihar.
Hakimin Lambata Mohammed Abdulsafur ya rasu a asibiti a cikin makon jiya a dalilin raunin da ya ji bayan wasu matasa sun bi shi har gida sun lakada masa dukan tsiya.
Kakakin rundunar Wasiu Abiodun ya ce ‘yan sanda sun kama wadannan mutane ne a binciken gid-gida da suka yi.
Ya ce wadanda rundunar ta kama sun hada da Umar Ilyasu Sarki, mai shekaru 37, Musa M. Musa Mai shekaru 47, Yakubu Bissala Dan shekaru 23, Hussaini Mohammed dan shekaru 18, Usman Habibu mai shekaru 40 da Ibrahim Umar mai shekaru 45.
Saura sun hada da Ismaila Mohammed mai shekaru 38, Ademola Okunola mai shekaru 51, Ilyasu Dantani dan shekaru 28, Yakubu Mohammed dan shekara 35, Yusuf Sarki mai shekaru 49, Atiku Mohammed dan shekara 21, Adamu Yusuf mai shekaru 46 da Bashir Moh’d dan shekara 27.
Mutanen sun bayyana wa jami’an tsaro cewa dama can akwai rashin jituwa tsakanin hakimin Lambata da Umar Ilyasu Sarki inda yake cewa sauran dakatai 37 dake karamar hukumar na goyan bayan sa ne ba shi hakimin ba.
Sun kuma ce baya ga su akwai wasu mutane da suke aikata mummunar abin tare da basu shiga hannu ba.
Wadannan mutane sun hada da Umar Sarki, Dauda Umar Sarki, Abdulkarim Dantani, Zubairu Moh’d, Zayanu Ladan da Jibril Garba.
Abiodun ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike domin kamo wadannan mutane.
Discussion about this post