Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya mika kokon barar sa ga gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele da ya wa Allah ya tsawaita kwanakin dakatar da kashe tsoffin kudi da aka kyayyade ranar 31 ga Janairu ranar kashe ta karshe a kasar nan.
Duk da kiraye-kirayen da ‘yan Najeriya da suka hada da majalisar dattawa na CBN ya kara wa’adin zuwa ranar 30 ga watan Yuni, CBN ya ya kafe a ranar 31 da ya saka tun a farko cewa babu gudu babu ja da baya.
Buni a cikin wata sanarwa ta bakin mai magana da yawunsa Mamman Mohammed ya bukaci babban bankin na CBN da ya yi wa al’ummar jihar rangwame na musamman ko kuma ya yi wani tsari na daban, musamman mutanen da ke zaune a karkara.
Buni ya ce kananan hukumomi 4 ne cikin 17 ke iya gudanar da harkokin banki a jihar saboda haka wa’adin ya yi matukar kadan.
“Wasu daga cikin bankunan da ke da rassa a kananan hukumomi sun rufe rassan a daidai lokacin da ake fuskantar kalubalen tsaro na Boko Haram amma har yanzu ba a bude su ba duk da saukin tsaro da aka samu a jihar”.
“Ya kamata CBN ya yi la’akari da haka sannan ya sassauta dokar ga musamman irin wadannan wurare masu bukatu na musamman don kaucewa sanya su cikin wadanda za su yi asarar kudadensu.
“Tsorona shine har sai fa an gaggauta yin wani abu, mutane da yawa ba za su iya canja kudaden su ba ko kuma ma su ajiye su a asusun ajiya kafin wannan wa’adi da hakan zai sa su rasa kudaden su na halal.
Discussion about this post