Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami, ya bayyana cewa bai karɓe shari’ar tuhumar tsohon Gwamnan Jihar Gombe Danjuma Goje daga hannun EFCC don don ran sa ba.
Da ya ke amsa tambayoyin PREMIUM TIMES a wata tattaunawar musamman da aka yi da shi kwanan nan, Malami ya ce Sashe na 174 (1a) da sauran wasu ayoyin cikin sashen sun ba shi ƙarfin ikon karɓe duk wata shari’a da ke a gaban kotu, idan yin hakan shi ne mafi alheri ga al’ummar ƙasa baki ɗaya.
Ya bayyana haka ne yayin da PREMIUM TIMES ta ƙalubalance shi cewa ana zargin EFCC ta janye hannun ta daga ci gaba da shari’ar Goje daidai lokacin da aka kusa yanke masa hukunci, don a sakar masa mara, shi kuma Gojen sai ya janye daga takarar shugabancin Majalisar Dattawa da a lokacin ya fito ya na yi shi da Ahmad Lawan, a 2019.
Idan ba a manta ba, EFCC ta janye daga tuhumar da ta ke yi wa Goje kan zargin satar naira bilyan 25 lokacin ya na Gwamnan Jihar Gombe.
A lokacin dai EFCC ta gurfanar da Goje ne a Babbar Kotun Tarayya da ke Jos, a gaban Mai Shari’a Badamasi Qadri, kuma har lula Kotu Ɗaukaka Ƙasa a kan tuhuma biyu daga cikin tuhumomi barkatai da aka yi wa Goje.
Kwatsam, ranar 7 Ga Yuli, 2019, ƙasa da kwanaki huɗu kafin zaɓen Shugaban Majalisar Dattawa, sai EFCC ta bayyana cewa ta janye tuhumar da ta ke yi wa Goje ta zargin satar naira biliyan 25.
EFCC ta bayyana haka ne kwana ɗaya bayan Goje ya ziyarci Shusba Muhammadu Buhari a fadar sa.
Bayan janyewar, Kakakin EFCC na lokacin, Tony Orileye, ya shaida cewa EFCC ta janye hannun ta daga ƙarar da ta gurfanar da Goje, saboda Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami ya amshe tuhumar daga hannun hukumar.
Shi dai Malami ya ce wa PREMIUM TIMES hakan da ya yi bai saɓa doka ba, kuma ba ya yi ba ne don son kan sa.
A tattaunawar dai Malami ya bayyana yadda Gwamnatin Buhari ta yi rawar gani a yaba a fannin shari’a, cin hanci, rashawa da sauran fannoni.
Discussion about this post