Kungiyar Dattawan Arewa ACF ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele da kakkausar murya su gaggauta janye maganar dakatar da kashe tsoffin takardun naira da ya ke neman jefa kasa cikin ruɗani.
Gwamnan babban banki CBN, da shi kansa shugaban kasa Muhammadu Buhari sun bayyana cewa lallai ba za a ɗage ranar da gwamnati ta saka na daina amfani da tsoffin rakardun kudin a Najeriya ba.
Ranar 31 ga Janairu ne gwamnati ta saka ranar ƙarshe da za a kashe tsoffin takardun kuɗi na naira 200, 500 da 1000.
Kungiyar ACF ta gargaɗi gwamnatin Buhari cewa idan ta ci gaba da cewa lallai kamar yadda ta faɗi ranar 31 ne za a dakatar kashe tsoffin takardun kuɗi, kasa zai afka cikin ruɗanin da bata taɓa shiga ba, domin kuwa talakawa ba samu waɗannan kuɗaɗe ba
” Domin kuwa babu sabbin kuɗi a bankunan da CBN ke cewa ta raba wa sabbin takardun kuɗin. Har yanzu da muke yi maka magana, tsoffin kuɗi su kan su bankuna ke badawa idan kaje cire kuɗi.
” Sannan kuma a nan ana cewa wai an wadata bankuna da sabbin kuɗi bayan su ba su bayar wa.
” Sarkin Musulmi Abubakar Saad da kan sa ya faɗi wa gwamnan babban bankin Najeriya cewa maganan sabbin takardun kuɗi zai kawo matsala a kasa ganin har yanzu wasu a kauyuka ba su san da maganar ba, ballantana su ga sabbin kuɗin har su kashe su.
” Babu makawa cewa idan har aka ce dole ranar 31 ga wata za daina kashe tsoffin naira, to lallai z a samu ruɗanin gaske da zai iya jefa kasa ciki ruɗu da tashin hankali. Wannan ko shakka babu domin mutane fa za su fada cikin halin ƙaƙanikayi.
Discussion about this post