Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta ce ba gaskiya ba ce wani rahoto da ya nuna cewa hukumar ta kai Shugaban INEC Mahmood Yakubu ƙara kotu, dangane da bayyana kadarorin da ya mallaka.
Kakakin DSS, Peter Afunanya ya ce rahoton da ya nuna haka bai bayyana yadda labarin ya ke ba, don haka DSS ba ta maka Shugaban INEC kotu ba.
Ya ce wasu masharranta ne masu son ɓata lokacin kotu domin su haddasa fitina a ƙasar nan, tare da kawo saɓani a tsakanin hukumomin gwamnatin tarayya.
Takamaimen labarin dai yadda ya ke shi ne, Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ce ta yi fatali da wata ƙara da wani mutum mai suna Somadina Uzoabaka ya kai Antoni Janar kuma Ministan Harkokin Shari’a, Abubakar Malami da Shugaban INEC, Mahmood Yakubu.
Uzoabaka ya roƙi kotu ta umarci Yakubu ya sauka daga shugabancin INEC, har sai an kammala binciken da DSS da wasu hukumomi za su yi masa, dangane da yadda ya ce wai Yakubu bai bayyana kadarorin sa bisa ƙa’ida ba.
Sai dai kuma Mai Shari’a Maryam Hussain ta yi fatali da ƙarar, inda ta yanke hukuncin cewa Shugaban INEC ya bayyana kadarorin sa bisa ƙa’ida kamar yadda dokar ƙasa ta gindaya masa.
Haka kuma Mai Shari’a ta umarci DSS ko wata hukumar tsaro kama Yakubu ko bincikar sa, tunda bai aikata laifin komai ba.
A kan haka ne Hukumar DSS ta bakin Peter Afunanya, ta ce ita ba ta da wata matsala da Shugaban INEC, ba ta maka shi kotu ba, kuma ba ta yi wata niyya ko tunanin kama shi ko binciken sa ba.
Afunanya ya ce hukumar su a shirye ta ke ta bai wa INEC goyon bayan tabbatar da an yi zaɓen 2023 lami lafiya.