Wani jigon APC mai suna Tunji Abayomi, ya ce “kada ‘yan Najeriya su tsaya ɓata lokacin neman mutum nagari wajen neman wanda zai gyara Najeriya, domin wannan aikin sai gogaggun masu saɓon Allah.”
Abayomi, wanda shugaba ne a Jami’ar Adekunle Ajasin da ke Ondo, ya ce talauci ne ya rigaya ya yi wa jama’a katutu a ƙasar nan. Don haka su tsaya kawai su zaɓi wanda zai iya yalwata jama’a da dukiya, su daina daddagewa su sai mutumin kirki kuma nagari mai tsoron Allah za su zaɓa.
Ya bayyana haka a wata tattaunawa da shi a ranar Talata, a gidan talabijin na Channels TV.
“Ba masu iya fitar mutane daga aikata zunubi, sai waɗanda suka goge da yin ƙaurin suna wajen aikata manyan zunubai. Saboda su suka san illolin zunuban da su ka aikata.” Inji Abayomi, wanda lauya ne.
Idan za a iya tunawa, wasu fitattun ‘yan takara na fama da kwatagwangwamar zargin su da satar dukiyar al’umma.
Amurka ta taɓa ƙwace dala 460,000 daga hannun ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu saboda kama shi da baranƙyanƙyamar laifin safarar muggan ƙwayoyi a ƙasar, cikin 1992.
Shi ma ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar ya na fuskantar zargin karkatar da maƙudan kuɗaɗe a wani gwanjangwalamar harƙallar sayen Motocin Ayyukan Musamman, cikin 1998, lokacin da ya na Mataimakin Shugaban Ƙasa a ƙarƙashin mulkin Olusegun Obasanjo.
PREMIUM TIMES ta taɓa buga labarin yadda Peter Obi, ɗan takarar LP ya yi amfani da kamfanin Shell, ya karkatar da maƙudan kuɗaɗe ƙasar waje, domin ya kauce wa biyan ɗimbin kuɗaɗen haraji a nan cikin gida Najeriya. Kuma lokacin da zai cika fam na rantsuwar yawan kadarorin sa, kamar yadda doka ta tanadar, bai bayyana kadarorin na sa na waje ga INEC ba, kamar yadda doka ta tanadar.
Abayomi ya ce don haka, “babu yadda za a yi a Najeriya a safe ma’asumin da ba ya aikita saɓo a ƙasar nan, ballantana a ce sai shi ne kaɗai zai iya gyara Najeriya.”
Dalili kenan ya ce “abin da ƙasar nan ke buƙata kawai shi mutum wanda ya ke da hikima irin ta mutanen dauri, ba wai salihin mutumin da ba ya aikata saɓo ba.”
Ya ce, “a tuna fa duk wannan ruguntsumi da karafkiyar da ake yi, a duniya ake, ba a lahira ko aljanna ba. Don haka ɗan duniya ne kawai zai iya yin wannan gyara, ba mai ‘zuhudun’ gudun duniya ba.”
Discussion about this post