Gwamnatin jihar Katsina ta kori hakimin Makaman Katsina Idris Sulefor da ake zargi ya na da ala’ka da ‘yan bindiga a jihar.
A wata wasika mai dake dauke da kwanan wata 19 ga Janairu 2023 Kauran Katsina wanda shine hakimin Rimi, Aminu Nuhu-Abdulkadir ya ce gwamnati ta kori hakimin ne bayan kwamitin da gwamnati ta nada domin gudanar da bincike kan hakimin ta gano ya aikata laifin da ake zargin sa da su.
“Bayan wata wasika da majalisar masarautar ta samu daga ofishin sakataren gwamnatin jihar mai lamba SEC/54/Vol.VI/1416 inda gwaman jihar ya tabbatar da zargin da ake yi maka gaskiya ne wanda suka nemi su hana zaman lafiya a masarautar. A dalilin haka ya sa gwamnati ta sauke ka daga matsayin Hakimin Bakori. Inji Abdulkadir.
Kakakin masarautar Ibrahim Bindawa ya tabbatar da haka wa PREMIUM TIMES.
Zuwa yanzu Makaman Katsina ya shiga jerin sarakunan da gwamnati ta Kore su daga sarauta bayan ta gano cewa suna da ala’ka da ‘yan bindigan da suka rika kisa da yin garkuwa da mutane a yankin Arewacin kasar nan.
A jihar Zamfara gwamnati ta kori sarkin Zurmi Atiku Abubakar, sarkin Dansadau Hussain Umar da hakimin Birnin Tsaba Sulaiman Ibrahim bayan an gano suns ala’ka da ‘yan bindiga a jihar.
Discussion about this post